Rahotanni sun kawo cewa gwamnatin jihar Kano karkashin jagorancin Abba Kabir Yusuf wanda aka fi sani da Abba Gida-Gida ta soke gaba daya lasisin yan masa'antar shirya fina-finan Hausa ta Kannywood.
Shugaban hukumar tace fina-finai ta jihar Kano, Abba Almustapha, ya bayyana dalilan da suka sanya gwamnatin jihar daukar wannan makali. Legit ya wallafa.
Abin da ya sa muka soke lasisin yan Kannywood - Abba El-Mustapha
A hirar da ya yi da Freedom Radio, Almustapha ya ce sun dauki wannan matakin ne domin tsaftace harkar fim gaba dayan ta domin a cewarsa ana abubuwa babu tsari a masana'antar ta fina-finai.
Ya ce a halin da ake ciki a yanzu kowa a masana'antar yana amsa sunar jarumi, furodusa, mai daukar hoto ba tare da wani tsari ba saboda haka soke lasisin zai sa su samu damar yi wa lamarin tufkar hanci.
A cewarsa da wannan mataki da suka dauka, yanzu sai sun tantance mutum sun tabbatar da nagartarsa, sun tabbatar da ya cancanta kafin ma su ba shi lasisin aiki.
Har ila yau, shugaban hukumar tace fina-finan ya ce wannan zai sake basu damar sanin ta inda mutum ya shigo masana'antar ta yadda koda wani abu ya faru a gaba za su san ta ina za su faro ta.
A bangaren tallace-tallace, Almustapha ya ce akwai masu tallace-tallacen magunguna wanda a yanzu suna so sai an tantance magungunansu da kuma maganganun da suke amfani da shi na batsa da sauransu maganganu da bai kamata al'umma su ji ba.
Har wayau, a cikin bidiyon jawabinsa, shugaban hukumar tace fina-finan ya ce an soke lasisin yan gidajen gala ta yadda sai sun zo sun sabonta rijistarsu domin su kawo tsafta da kawar da bara gurbi a cikinsu.
Ya kuma tabbatar da cewar ba wai sun kawo wannan matakai don takurawa mutanen masana'antar ba ya ce suna yi ne don inganta sana'ar.
Yan Kannywood za su dara a gwamnatin Abba Kabir Yusuf, inji Abba Al-Mustapha
A baya mun ji cewa fitaccen jaruminnan na masana'antar Kannywood, Abba Ruda, wanda aka fi sani da Abba El-Mustapha, ya bayyana cewa yan wasan fina-finan Hausa za su dara a wannan gwamnati ta Abba Gida Gida.
Ya bayyana hakan a wata hira da ya yi da gidan rediyon Freedom da ke Kanon Dabo.
Published by isyaku.com