Gwamna Lawal ya rage ma'aikatun Gwamnatin Zamfara daga 28 zuwa 16


Gwamna Dauda Lawal na Zamfara a ranar Alhamis, 6 ga watan Yuli, ya rattaba hannu kan dokar rage ma’aikatun jihar daga 28 zuwa 16 domin inganta maaikatun Gwamnati.

Babban Daraktan yada labarai da sadarwa na ofishin gwamnan, Malam Nuhu Anka ne ya bayyana hakan.

Lawal ya ce ya fara sake fasalin ma’aikatu da hukumomin gwamnati domin rage tsadar tafiyar da harkokin mulki da inganta samar da ayyuka masu inganci.  Haka kuma zai shafi sauran ma’aikatun gwamnati, hukumomi da nufin tabbatar da ingancin aiki.

Ya tabbatar da cewa za a nada mutanen da suka tabbatar da gaskiya da aiki tukuru a ma’aikatu domin inganta harkokin gudanar da mulki da zai bunkasa jihar. 

Published by isyaku.com

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN