Daya daga cikin Yan sandan da aka kashe |
Wasu ‘yan bindiga dauke da makamai sun kashe ‘yan sanda hudu a wani hari da suka kai a karamar hukumar Bungudu a jihar Zamfara.
An ce jami’an sun dora shingayen binciken ababen hawa ne a kan titin Bungudu-Gusau lokacin da ‘yan bindigar suka yi musu kwanton bauna tare da bude musu wuta a daren ranar Litinin, 10 ga watan Yuli, 2023.
Wani mazaunin garin Bungudu mai suna Ibrahim Bungudu ya ce ‘yan bindigar sun kuma harbe mutum daya a kauyen Tagero da ke karkashin gundumar Furfuri a karamar hukumar Bungudu.
Bungudu ya kara da cewa ‘yan bindigar sun kuma yi awon gaba da wasu shanu na mazauna kauyen Tagero.
“’Yan bindigar sun yi wa ‘yan sanda kwantan bauna a kan hanyar Gusau-Bungudu kusa da kamfanin Nabature inda suka kashe mutane hudu, sun kuma yi awon gaba da shanu da dama a kauyen Tagero da ke karkashin gundumar Furfuri, an harbe mutum daya a hannu a kauyen,” inji shi.
Wani mazaunin garin Bungudu, Usman Bungudu, ya ce lamarin ya faru ne da misalin karfe 12 na dare a lokacin da ‘yan sandan suka dora shingayen binciken ababen hawa a kan hanyar Gusau. ‘Yan fashin dai sun yi musu kwanton bauna ne suka harbe su; sun gudu ne bayan sun kashe ‘yan sanda hudu.”
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Zamfara, ASP Yazid Abubakar, wanda ya tabbatar da faruwar harin a safiyar ranar Talata, ya ce ‘yan ta’addan sun yi wa jami’an kwanton bauna ne a lokacin da suke aikin sintiri a kan hanyar.
"Uku daga cikin 'yan sandan da suka mutu jami'an rundunar ne, yayin da daya kuma jami'in tsaro ne," in ji PPRO.
Ya ce wannan abin takaici ba zai sa rundunar ta yi kasa a gwiwa wajen samar da tsaro a jihar ba.
Published by isyaku.com