Sakataren jam'iyyar APC na ƙasa, Sanata Iyiola Omisore, ya fice daga wurin taron gaggawa na kwamitin gudanarwa (NWC) ba tare da ya saurari 'yan jarida ba. Legit ya wallafa.
Jaridar Daily Trust ta tattaro cewa taron NWC na APC ta ƙasa na gudana yanzu haka a babbar sakatariyar jam'iyya mai mulki da ke babban birnin tarayya Abuja.
Sanata Omisore na É—aya daga cikin mambobin kwamitin gudanarwa NWC da suka isa wurin taron a kan lokaci.
Sai dai jim kaɗan bayan isa wurin, aka ga sakataren APC na ƙasa, Sanata Omisore ya shiga mota ya bar sakatariyar ba tare da ya yi hira da 'yan jarida ba.
Wannan ne taro na farko tun da aka ji cewa Sanata Abdullahi Adamu ya yi murabus daga matsayin shugaban APC na ƙasa.
Meyasa aka hana Omisore shiga wurin taron?
Rahoton Vanguard ya nuna cewa kiri-kiri aka hana Sakataren APC shiga ɗaƙin taron NWC, wanda mataimakin shugaban jam'iyya na shiyyar arewa, Abubakar Kyari, ke jagoranta.
Sanata Omisore wanda ya isa Sakatariyar da wuri amma duk da haka ya taras mataimakinsa ya kwace wurin fakin din mota na sakataren APC.
Omisore, wanda ya bar Sakatariyar jim kaÉ—an bayan isarsa, ya ce ya zo ne domin gana wa da Abdullahi Adamu. A cewarsa bai san me ya hana Adamu zuwa sakatariyar ba.
Sakataren tsare-tsaren APC, Nze Chidi Duru, ya ce mambobin NWC na tsammani Omisore zai bi sawun Adamu, ya miƙa takardar murabus daga muƙamin sakatare.
Published by isyaku.com