Yadda Saurayi Da Budurwarsa Suka Sayar Da Jinjirinsu Don Siyan Kwayoyi


Jami'in hukumar da ke yaÆ™i da fataucin bil'adama ta jihar Edo, sun cafke wani mai suna Anthony Igbinogun dan shekaru 48, tare da budurwarsa Joy Umukoro, ‘yar kimanin shekara 28.

An kama saurayin da budurwar tasa ne bisa laifin sayar da jaririnsu ɗan wata ɗaya domin samun kuɗin shan ƙwayoyi, kamar yadda jaridar The Punch ta ruwaito.

Haka nan kuma, jami'an sun kama waÉ—anda ake tuhumar tare da wata abokiyarsu mai suna Precious James, yar kimanin shekaru 26, da ta taimaka wajen haÉ—asu da wanda ya sayi jaririn, a Fatakwal ta jihar Ribas.

A kan kudi N1.7m ne mutanen biyu suka sayar da jaririn

A zantawarta da 'yan jarida a Benin babban birnin jihar Edo, shugabar sashin bincike na hukumar yaƙi da fataucin dan adam ta jihar Edo, Abigail Ihonre, ta ce an sayar da jaririn a kan kuɗi naira miliyan 1.7.

Ta kuma ƙara da cewa jami'ansu na ci gaba da gudanar da bincike don ceto jaririn ɗan wata ɗaya, tare da cafko mutumin da ya saye shi.

A cewar Ihonre:

“Binciken da muka gudanar ya nuna cewa, Joy Umukoro, ta haifi jaririn ne a watan Afrilun 2023, sai suka haÉ—a baki ita da saurayinta don su sayar da jaririn nasu kan naira miliyan 1.7. Ta kuma amsa laifin sayar da jaririn da ake tuhumarta da shi.”

“Ana ci gaba da gudanar da bincike kan lamarin domin kamo waÉ—anda suka sayi jaririn domin a gurfanar da su a gaban kotu daga nan zuwa ranar Litinin 26 ga watan Yuni, 2023, saboda ya zamto cewa duk wanda ke da hannu a ciki ya fuskanci fushin doka kan laifukan da ya aikata.”

Saurayin da budurwar sun bayyana dalilinsu na siyar da jaririn na su


WaÉ—anda ake zargin sun ce sun aikata wannan É—anyen aikin ne saboda ba za su iya kula da jaririn ba.

Sai dai jami'ar hukumar yaƙi da fataucin mutanen ta musanta iƙirarin da suka yi.

Ta ce suna ta'ammuli da miyagun kwayoyi ne, wanda hakan ya sa ba za a su iya É—aukar dawainiyar jaririn ba, inda ta ce ganin haka ne ya sa suka yanke shawarar sayar da shi.

Jami'ar ta ƙara da cewa wannan matakin da suka ɗauka babban kuskure ne da zai iya lalata musu rayuwarsu.

Jaridar Independent ta ruwaito Abigail na cewa duk wanda ba zai iya É—aukar É—awainiyar É—an da ya haifa ba, ya kawo musu shi ofishinsu maimakon siyar da shi.

By/Daga - Click/Latsa isyaku.com

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN