![]() |
Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya bada tabbacin cewa ana shirin samar da ababen more rayuwa don dakile illar cire tallafin man fetur.
Ya yi wannan jawabi ne a yayin wani taron tattaunawa da ‘yan Najeriya mazauna Faransa da makwaftaka da kasashen Turai, a gefen taron sabuwar yarjejeniyar hada-hadar kudade ta duniya da aka yi a babban birnin kasar Faransa, Paris.
Shugaban a jawabinsa na bude taron ya ce zamanin tallafin ya wuce ne saboda babu kasafi a cikin kasafin kudi. Jaridar The Nation to rahoto.
Dangane da yadda ya shawo kan kungiyar Labour ta tsayar da zanga-zangar da aka shirya yi kan cire tallafin, ya ce:
“Kuna son karin kudi a cikin abin dogaro, sufuri me kuke zanga-zangar? Kuna raba wani É“angare na tallafin? idan kun yi zanga-zanga ni ma zan bi ku in yi zanga zangar. Babu zanga-zanga.
"Za mu samu Palliative amma dole ne mu ajiye kudin domin tanadi," in ji shi.
By/Daga - Click/Latsa isyaku.com