Tsohon shugaban kasar Amurka Donald Trump ya ki amsa laifuka 37 da gwamnatin tarayya ta tuhume shi da aikatawa yayin da aka fara sauraron karar mai cike da tarihi a birnin Miami na jihar Florida.
Trump, wanda zai cika shekaru 77 a gobe, ya bayyana a gaban Kotun Amurka ta Wilkie D. Ferguson tare da lauyoyi Chris Kise da Todd Blanche.
Yana fuskantar tuhume-tuhume da yawa na gwamnatin tarayya sakamakon zarge-zargen da ake masa da kuma boye wasu manyan takardu bayan ya bar fadar White House a watan Janairun 2021.
Daga cikin takardun sirrin da ya kwashe har da wadanda suka shafi makamashin nukiliya.
An kuma gurfanar da mai taimaka wa Trump Walter Nauta a makon da ya gabata kan wasu laifuka guda shida masu alaka. An tuhume shi da taimakawa Trump wajen boye takardun a wurin shakatawa na Mar-a-Lago, shi ma a Florida.
BY isyaku.com