Abubuwa 7 da Suka Hana Abdulaziz Yari Zama Sabon Shugaban Majalisar Dattawa

Sanata Abdul-Azeez Yari

A wannan rahoto, Legit.ng Hausa tayi nazarin abubuwan da su ka jawo tsohon Gwamnan Zamfara, Abdulaziz Yari ya gagara samun nasara.

Ga wasu daga cikin dalilan da ake gani

1. Yadda APC ta ware kujeru


Shugabannin Jam’iyyar APC sun yarda cewa shugaban majalisar dattawa ya fito daga Kudu maso kudu, sai a ba Arewa maso yamma kujerar mataimaki.

Abdulaziz Yari wanda ya fito daga yankin Arewa ta yamma ya gamu da cikas tun farko domin idan aka yi wa APC biyayya, Barau Jibrin zai samu mukami.

2. Fadar shugaban kasa


An ji yadda Sanata Ali Ndume ya ke bada labarin irin gudumuwar da Bola Ahmed Tinubu ya bada saboda ganin Godswill Akpabio ya lashe zaben na jiya.

Mai girma shugaban kasa ya yi yadda ya iya har ana gobe zabe domin ganin Yari bai kai labari ba. Ka da a manta, mai dakinsa Sanatar Legas ce tun 2011.

3. Yaushe ka zo Majalisa?


Daga David Mark zuwa Ahmad Lawan, duka shugabannin majalisar da aka yi sun dade kafin su shiga takara, shi kuwa Yari sai yanzu aka rantsar da shi.

Godswill Akpabio ya yi shekara hudu a majalisa, akwai abokan aikinsa a cikin Sanatocin.

4. Kashim Shettima bai tare da Yari


Baro-baro aka ji Kashim Shettima ya fito yana goyon bayan Kiristan kudu a zabe, ya nuna bai dace a sake samun wani Musulmi ya rike mukami na uku a kasar.

Mataimakin shugaban kasar ya wakilci Borno ta tsakiya, ya sa kan aikin Majalisa.

5. Rasa mulkin Zamfara


Mulkin jihar Zamafara ya bar hannun Jam’iyyar APC a zaben 2023, wannan ya jawo tsohon Gwamnan bai da wanda zai ba shi kwarin gwiwar takara.

Sabon Gwamna, Dauda Lawal Dare ya na mulki ne a PDP, hakan ya jawowa Yari karin matsala.

6. Janyewar Uzor Kalu da kokarin Hope Uzodinma


Ana tunanin rade-radin hakura da takara da Orji Uzor Kalu ya yi, ya taimaka wajen rage kuri’un da ya kamata Abdulaziz Yari ya samu daga kudu maso gabas.

Idan rahotanni sun tabbata, Gwamnan Imo ya taka rawar gani sosai wajen janye wasu masu goyon bayan Alhaji Yari da farko, su ka zabi Godswill Akpabio.

7. Zargin da ke kan wuyan Yari


Watakila zargin da aka rika jifan zababben Sanatan da shi ya yi tasiri, har ya dage wajen wanke kan shi. An zargi wasu 'yan takaran da amfani da dukiya.

Shi ma Godswill Akpabio bai rasa kashi a gindinsa, amma kusan babu wanda ke magana a kai.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN