Rushewar ginin Kano: Hukumomi sun tabbatar da mutuwar mutum guda, an ceto uku da ransu

Rugujewar gini a Kano

Hukumar kashe gobara ta jihar Kano tq tabbatar da mutuwar mutum daya sakamakon rugujewar otal din Daula dake jihar.

 Mai magana da yawun hukumar Saminu Yusif ya ce an ciro gawar wani mutum daya da ya makale a karkashin tarkacen ginin da ya ruguje sakamakon haka ya mutu. Jaridar vanguard ta rahoto.

 Yusif ya ce an ceto wasu jimillar mutum uku da ransu.

 “Ya zuwa yanzu, mun ceto mutane hudu da abin ya shafa.  An ceto uku a raye yayin da aka tsinci gawar dayan.  Tuni dai aka kwashe gawar zuwa asibitin kwararru na Murtala Muhammad.

 “A cewar mutanen da ke kusa a lokacin da lamarin ya faru, sun ce har yanzu akwai sauran mutanen da suka makale a karkashin tarkacen.  Don haka mutanenmu suna ci gaba da bincike ko sun sami wani wasu.”

 Lamarin dai ya faru ne da misalin karfe 1:00 na rana, inda aka ce ‘yan gongo masu neman karafa daga baraguzan ginin sun ruguza rabin ginin wanda kwatsam ya ruguje a kansu suka makale.

 A nasa bangaren, kwamishinan ‘yan sandan jihar Kano, CP Mohammed Usaini Gumel da ya ziyarci wurin da lamarin ya faru, ya ce sun killace ginin, amma ‘yan gongo sun bijirewa lamarin inda suka kutsa ginin ya ruguje suka makale.

 CP Gumel ya yi kira ga iyaye da su ja kunnen yayan su da su daina shiga gine ginen da aka ruguje a jihar ya na mai bayanin cewa kawo yanzu hukumar Yan sandan jihar ta kama mutane 106 da ake zargi da wawure kadarori daga gine-gine da aka ruguje a jihar kuma nan ba da jimawa ba za a gurfanar da su a gaban kotu.

 Manajan Daraktan Hukumar Tsare-Tsare da Cigaban Birane ta Jihar Kano, KNUPDA, Architect Ibrahim Yakubu, ya ce gwamnati ta fara gina katanga a kewayen duk ginin da aka ruguje domin a samu cikakken tsaro daga masu kutse don kwasar dukiya, don haka ana zaton a dakile masu kutse su shiga ginin da aka rusa.  saboda hadurran da ke tattare da ita.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN