Bincike mai zafi: DSS ta yi gum kwana shida bayan cafke Emefele


Gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN) da aka dakatar, Godwin Emefiele ya kwashe kwana na shida a hannun hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) yayin da hukumar ta yi gum kan ko za a gurfanar da shi kotu ko a’a.

 Hukumar DSS ta kama Emefiele da yammacin ranar Juma’ar da ta gabata jim kadan bayan dakatar da shi da shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yi. Jaridar The Nation to rahoto.

 A ranar Asabar, mai magana da yawun hukumar DSS, Peter Afunanya, ya tabbatar da cewa Emefiele na tsare a hannun su saboda wasu dalilai na bincike.

 Ko da yake bai bayyana dalilan ba, amma an tattaro cewa wahalar Emefiele na da alaka da zarge-zargen ta’addanci da rashin kudi a babban bankin.

 A watan Disambar da ya gabata ma’aikatar ta yi yunkurin samun umarnin kotu na kama Gwamnan CBN bisa zargin “ayyukan bayar da tallafin ta’addanci, ayyukan zamba da kuma laifukan tattalin arziki na tsaron kasa.”

 Sai dai hakan bai yi nasara ba saboda kotun ta yanke hukuncin cewa DSS din ba ta bayar da wata kwakkwarar hujja da za ta tabbatar da ikirarin da ta yi na cewa Emefiele na da hannu wajen bayar da kudaden ta’addanci da kuma laifukan tattalin arziki ba.

 Rahotanni sun bayyana cewa, ana sa ran hukumar za ta tunkari kotun a ranar Talatar da ta gabata domin samun umarnin ci gaba da tsare shugaban babban bankin na CBN domin samun damar gudanar da cikakken bincike.

 Sai dai har zuwa lokacin gabatar da wannan rahoto, ba a iya tabbatar da cewa an samu irin wannan odar ba.

 Hukumar ta DSS ta kuma gayyaci Mista Abdulrasheed Bawa, dakataccen Shugaban Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arziki Tu’annati (EFCC) a ranar Laraba.

 Afunanya, a wata sanarwa da ya fitar a yammacin ranar Laraba, ya ce Bawa na tsare.

 “Bawa ya iso sa’o’i kadan da suka wuce.  Gayyatar ta shafi wasu ayyukan bincike da suka shafi shi,” in ji Afunanya.

 Sai dai bai yi karin bayani ba

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN