Karin farashin lantarki wata mai zuwa da kashi 40, NLC ta gargadi Gwamnatin Najeriya

Kungiyar kwadago a Najeriya
Yan kungiyar kwadago a Najeriya

Ƙungiyar Kwadago ta Najeriya NLC ta yi kira ga gwamnatin tarayya ta jingine shirinta na yin ƙarin kuɗin wutar lantarki da kashi 40 cikin 100 cikin wata mai zuwa. BBC Hausa ya rahoto.

Cikin wata sanarwa da shugaban ƙungiyar Joe Ajaero, ya fitar, ya ce matakin zai ƙara wa 'yan ƙasar musamman talakawa ''wahalhalu da matsin da suke ciki''.

Kafofin yaɗa labaran Najeriya sun ruwaito hukumar kula da harkokin wutar lantarki ta kasar NERC na shirin ƙara kuɗin wutar daga ranar 1 ga watan Yuli mai zuwa.

A wani mataki na janye tallafin da gwamnatin ƙasar ke biya kan kudin wutar lantarkin.

BBC ta tuntuɓi hukumar ta NERC, don jin bahasinta kan matakin, to amma jami'in hulɗa da jama'a na hukumar Michael Faloseyi ya ce ba a ba shi izinin yin magana kan batun ba.

'Yan ƙasar da dama sun bayyana kaɗuwarsu kan matakin ƙarin kuɗin wutar lantarkin, suna masu fargabar cewar zai haifar musu da ƙarin matsin tatalin arziki.

A watan da ya gabata ne gwamnatin ƙasar ta sanar da matakin janye tallafin man fetur, lamarin da ya haddasa ƙaruwar farashin man fetur da na kayan abinci a faɗin ƙasar.


By/Daga - Click/Latsa isyaku.com

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN