DSS ta yi gargadi: Akwai yiwuwar barazanar harin ta'addanci lokacin shagulgulan Sallah - isyaku.com


Hukumar tsaron farin kaya, DSS ta ce ƴan ta’adda na shirin kai hare-hare a masallatan idi da wuraren shaƙatawa lokacin Sallah Babba.

Kakakin DSS, Dr Peter Afunanya ne ya sanar da haka a ranar Alhamis. Jaridar Aminiya ta wallafa.

Don haka ya  buƙaci duk masu kula da wuraren taruwar mutane irinsu kasuwanni da wuraren shaƙatawa da su kai rahoton duk motsin da basu amince da shi ba ga jami’an tsaro.

Ya ce DSS ta ƙwato abubuwa masu fashewa daga hannun waɗanda take zargin ƴan ta’adda ne.

Dr Afunanya ya ce hukumar ta kuma  kama makamai da albarusai daga wurin ƴan ta’adda a kan hanyar Abuja – Keffi cikin jihar Nassarawa.

By/Daga - Click/Latsa isyaku.com

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN