Jita-jitan kama Emefele da shan tambayoyi, DSS ta ce baya hannunta

Emefele and DSS operatives of Nigeria

Hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) ta ce tsohon gwamnan babban bankin Najeriya (CBN), Godwin Emefiele, ba ya hannun ta a halin yanzu.

 Shugaban kasa Bola Tinubu ya dakatar da Emefiele ne a ranar Juma’a, inda ya umarce shi da ya gaggauta mika ragamar tafiyar da harkokin ofishinsa ga Folashodun Adebisi Shonubi, mataimakin gwamnan ( Directorate) na CBN. Daily trust ta rahoto.

 Dakatar da shugaban kasar, a cewar wata sanarwa mai dauke da sa hannun sakataren yada labarai Willie Bassey, sakamakon binciken da ake yi a ofishinsa da kuma shirin yin gyare-gyare a bangaren hada-hadar kudi na tattalin arzikin kasar.

 Bayan sanarwar dakatar da Emefiele, an samu rahotannin kama shi da ‘yan sandan sirri suka yi amma hukumar DSS ta kasa amsawa lokacin da aka tuntube ta.

 Amma a wani sako da hukumar ta wallafa a shafinta na Twitter a safiyar ranar Asabar, ta ce: “A halin yanzu, Emefiele ba ya tare da DSS.”

 Sai dai hukumar DSS ta kasa yin karin haske kan ko an kama shi a baya.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN