Ƙungiyar ƙwadago ta ƙasa (NLC) ta bayyana shirin tsunduma cikin yajin aiki idan ba a cimma matsaya ba a tattaunawar da ta ke da gwamnatin tarayya kan cire tallafin man fetur da ƙara mafi ƙarancin albashi.
Kamar yadda Punch ta rahoto, za a ci gaba da tattaunawa tsakanin ƙungiyar ƙwadagon da gwamnatin tarayya domin samun mafita kan buƙatun da ƙungiyar ta gabatarwa da Shugaba Tinubu. Legit ya wallafa.
Ƙungiyar ƙwadagon ta buƙaci gwamnatin tarayya ta ƙara mafi ƙarancin albashin ma'aikata daga N30,000 zuwa N150,000 saboda cire tallafin man fetur.
A zaman da ya gabata wanda aka gudanar a tsakanin ɓangarorin biyu, shugaban ma'aikatan fadar shugaban ƙasa, Femi Gbajabiamila wanda ya wakilci gwamnatin tarayya, ya bayyana cewa sun cimma mafita guda bakwai domin rage raɗaɗin cire tallafin man fetur ɗin.
Ƙungiyar Ƙwadago ta yi barazanar shiga yajin aiki idan?
Da yake magana kafin zuwan ranar zaman da sake gudanarwa a tsakanin ƙungiyar ƙwadago da gwamnatin tarayya ranar Litinin, 19 ga watan Yuni, mataimakin shugaban ƙungiyar na ƙasa, Adewale Adeyanju, ya ce za su tsunduma yajin aiki idan gwamnati ta kawo wargi.
Ya bayyana cewa an gabatarwa da gwamnatin tarayyar buƙatu masu yawa daga ciki har da sake farfaɗo da matatun man fetur ɗin ƙasar nan.
Adeyanju, a ranar Lahadi, 18 ga watan Yuni ya bayyana cewa a shirye su ke su saurari abinda gwamnatin tarayyar za ta zo da shi, sannan idan bai cika abubuwan da su ke buƙata ba, za sƴ tsunduma cikin yajin aiki.
Dalilai 5 Da Yasa Yajin Aikin NLC Kan Man Fetur Ba Zai Yi Nasara Ba
A baya rahoto ya zo kan dalilan da za su sanya yajin aikin da ƙungiyar ƙwadago ba zai yi nasara ba.
Daga cikin dalilan akwai rarrabuwar kai da ke a cikin ƙungiyar ƙwadagon da zargin siyasantar da lamuran ƙungiyar.
By/Daga - Click/Latsa isyaku.com