Gwamna Idris ya kaddamar da Majalisar dokokin Kebbi karo na 10 an zabi Kakakinta daga Zuru

Hon. Muhammed Usman Ankwai Zuru Speaker 10th Kebbi state House of Assembly

Gwamnan Jihar Kebbi Kwamared Dr. Nasir Idris Kauran Gwandu ya kaddamar da Majalisar Dokokin Jihar Kebbi karo na 10 a yau Alhamis. Shafin labarai na isyaku.com ya samo.

Hakan na kunshe ne a takarda da mai taimaka wa Gwamnan jihar Kebbi kan harkar watasa labarai Yahaya Sarki ya fitar ranar Alhamis a Birnin kebbi.

 Da yake karanta sanarwar da gwamna Idris ya yi a zauren majalisar, magatakardar majalisar, Suleman Shamaki, wanda ya jagoranci zaman majalisar ya shaida wa ‘yan majalisar cewa ya karbi sanarwar da gwamnan ya yi na kaddamar da majalisar.

 Ya sanar da cewa kundin tsarin mulkin tarayyar Najeriya ya baiwa gwamnan ikon bayar da shela kan kaddamar da majalisar dokokin jihar.

 A cewarsa, abin da sanarwar ta kunsa shine 'Akwai wani tanadi a sashe na 105 karamin sashe na 3 na kundin tsarin mulkin tarayyar Najeriya 1999 da aka yi wa kwaskwarima

 ' Cewa mutumin da aka zaba a matsayin gwamna yana da ikon gabatar da shela ga majalisar dokokin jihar nan take bayan an rantsar da shi .

 “Saboda haka, ni comrade Dr Nasir Idris, Kauran Gwandu Gwamnan Jihar Kebbi a bisa ikon da sashe na 105 karamin sashe na 3 na kundin tsarin mulkin kasa ya bani, don haka na sanar da cewa, za a yi zaman farko na majalisa ta 10 a zauren majalisar Assembly chamber, Birnin Kebbi ranar 8 ga watan Yuni, 2023 da karfe 11:00 na safe, in ji shi.

 Magatakardan ya tabo batun ‘yancin cin gashin kai na harkokin kudi na majalisar, inda ya ce an shawo kan lamarin, sai dai kawai ya bar majalisa da bangaren zartarwa su hada kai don aiwatar da su.

 A halin da ake ciki, yayin da Gwamna Idris ya kaddamar da majalisa ta 10, 'yan majalisar dokokin jihar sun zabi Hon.  Muhammad Usman, Ankwai Zuru daga mazabar Zuru a matsayin sabon kakakin majalisar.

 An zabi sabon kakakin ne bayan da Hon.  Adamu Muhammad Birnin Yauri da Hon Muhammad KK Augie ya goyi bayansa tare da gagarumin goyon baya daga ‘yan majalisar.

 ‘Yan majalisar dokoki ta 10 na jihar Kebbi sun kuma zabi Muhammad Samaila daga mazabar Bagudo a matsayin mataimakin kakakin majalisar.

 Bayan bikin kaddamarwar ne 'yan majalisar dokokin jihar Kebbi suka kai ziyarar ban girma ga gwamnan jihar Kebbi Dr.  Nasir Idris, Kauran Gwandu a Government House, Birnin Kebbi.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN