Da duminsa: Wani Manajan banki ya kashe kansa kan lamunin bashin N1m

SEAP Micro-Finance Bank Saki mai shekaru 41, Sola Ogungbe ya kashe kansa

Wani manajan bankin SEAP Micro-Finance Bank Saki mai shekaru 41, Sola Ogungbe ya kashe kansa a gidan sa na Iseyin.

 An ce Ogungbe ya bai wa wasu kwastomomin da suka kasa biya bashin kudin.

 An ce wani ma’aikacin bankin ya kira matar Ogungbe a ranar Laraba da yamma saboda tsohon manajan ba ya zuwa wurin aiki kan matsalar bashin kudin da ya bayar ga kwastomoni. Jaridar The Nation to rahoto.

 Lokacin da matar ta isa gida don sanar da mijin nata kiran, matar ta tarar da gawarsa.

 Wani makusancin marigayin, wanda ya nemi a sakaya sunansa, ya ce marigayin ya yi kuskure ta hanyar kashe rayuwarsa a maimakon tattaunawa da abokansa kan lamarin.

 Ya ce: “Batun kashe kansa na dada tayar da hankali, Sola ya yi babban kuskure da ya kashe kansa saboda bashi, da a ce ya raba wa abokansa wannan batu, da wata kila wani ya kawo masa dauki.

 "Kowa yana fama da matsala ɗaya ko wani lamarin damuwa a rayuwarsa, amma idan ka tattauna da abokai mai yiwuwa za ka sami wani daga cikin abokai dazai taimaka maka". 

 An kai gawar marigayin zuwa garinsu da ke Omu-Aran a jihar Kwara domin binne shi.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN