Shahararren dan wasan kwaikwayo na gidan talabijin na Reality TV, Afeez Agoro Oladimiji, wanda aka fi sani da matsayin mutum mafi tsayi a Najeriya, ya mutu.
Jaridar the Nation ta tabbatar da cewa an binne Agoro a gidansa da ke unguwar titin Akoka.
An tattaro cewa an garzaya da Agoro asibiti a jiya bayan ya samu wasu matsaloli.
Rubutun karshe na Agoro a Facebook shine ranar 28 ga Mayu bayan ya farfado daga aiki da aka masa a gefen kwankwasonsa. .
Ya rubuta: "Na gode wa Allah Madaukakin Sarki da ya sa aka yi nasarar gudanar da aiki a yanzu lokaci ya yi da za a yi maganin."
Agoro yana farfadowa da aikin daaka yi masa tare da taimakon likitansa, Dokta Dike.
Kafin rasuwarsa, tsayin Agoro mai jan hankali a duk inda ya tafi. Yana da tsayi 7ft 4in.
Mazauna yankin Akoka/Bariga sun fara mika gaisuwar tasu.
Shugaban Akoka CDA, Segun Adesanya ya tabbatar da rasuwarsa.
Ya ce: “Afeez Agoro na zaune ne a kan titin al’umma kuma abin bakin ciki ne mun rasa wani matashi mai kwazo. Allah ya jikansa ya sa ya huta.
BY isyaku.com