Wani matashi Sulaiman Aliyu Mairubutu ya tallafa wa Marayu 50 da N5000 kowannensu a Unguwar Bayan Kara da ke garin Birnin kebbi ranar Lahadi 14 ga watan Afrilu 2023.
An gudanar da bikin bayar da tallafin a unguwar bayan Kara. An zakuko Marayu wadanda ke da kwarewar sana'ar hannu tun kafin wannan lokaci kuma aka yi amfani da wannan dama don tallafa masu.
Mata zalla da suka amfana da tallafin na yau sun sami Naira dubu biyar kowacensu (N5000) wanda ya bayar da jimillar tallafin Naira dubu dari biyu da hamsin.
Bikin ya sami halartar Hakimin Unguwar bayan Kara Malam Gide, da sauran manyan mutane da Yan siyasa.
Karin bayani na nan tafe....
Latsa kasa ka kalli Hotuna
BY isyaku.com
RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI