Ma'aikatan Gwamnatin jihar Zamfara sun gudanar da Sallar Idi na musamman don neman a biya su albashinsu


Wasu ma’aikatan gwamnati a jihar Zamfara sun gudanar da sallah ta musamman a masallacin Idi da ke Gusau babban birnin jihar a ranar Asabar.

 Ma’aikatan da suka yi dandazo a masallacin da misalin karfe 10 na safe sun nemi gafarar Ubangiji kan albashinsu. Daily trust ta rahoto.

 Ma’aikatan dai sun ce an biya su albashi na karshe a watan Janairu, kuma suna fuskantar wahala wajen biyan bukatunsu.

 “Da yawa daga cikinmu sun zama mabarata, ba mu iya cin abinci murabba’i daya a rana.  Don haka, wannan zaman addu’a, wata hanya ce ta musamman don sadaukarwa mai girma gwamna, shugaban ma’aikata, ‘yan majalisar tarayya da duk wanda abin ya shafa, Allah ya ba su ikon tausaya mana.

 “Mun sha wahala sosai saboda wannan gwagwarmaya, da yawa sun rasa rayukansu kuma ba ma son hakan.  Mun taru ne don neman taimakon Allah ga kowa da kowa,” in ji daya daga cikinsu da ya nemi a sakaya sunansa.

 Kokarin jin martanin gwamnatin jihar kafin shigar da wannan labari bai haifar da sakamako ba domin an kashe layin wayar kwamishinan yada labarai Ibrahim Dosara.


Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN