![]() |
Illustrative picture |
Rahotanni sun ce mutane da dama sun kone kurmus a wani hatsarin da ya faru a hanyar Lokoja zuwa Abuja a jihar Kogi.
Wani ganau ya ce hatsarin ya faru ne lokacin da wata tankar mai dauke da mai ta rasa yadda za ta yi ta yi karo da motoci daga wata hanya. Daily trust ta rahoto.
“Tankar na ci gaba da konewa tare da wasu motoci da dama da suka makale a cikin lamarin. Na ga bas guda biyu na kasuwanci da motoci suna ci da wuta. Jami’an tsaro da suka hada da jami’an hukumar kiyaye hadurra ta kasa (FRSC) sun yi namijin kokari wajen kashe gobarar tare da ceto fasinjojin da suka makale a cikin gobarar,” in ji wani Yusuf daga garin kotonkarfei.
A cewarsa, hadarin ya afku ne kai tsaye a gaban sakatariyar karamar hukumar.
Kwamandan hukumar kiyaye haddura ta kasa Stephen Dawlung ya shaida wa Daily trust cewa an tura jami’an hukumar zuwa yankin.
“Mutane da yawa sun makale a hatsarin . Har yanzu dai tankar na ci gaba da konewa, lamarin da ya haifar da kalubalen zirga-zirgar ababen hawa a kan manyan tituna a halin yanzu. Zan ba ku cikakkun bayanai, da zarar mun gama,” in ji shugaban FRSC.
BY isyaku.com
RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI