Hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa, EFCC, a jiya ta ce ta bankado shirin da wasu masu rike da mukaman siyasa suka yi na ficewa daga kasar bayan wa’adinsu na ranar 29 ga watan Mayu.
PEPs sun hada da gwamnoni, ministoci da kuma masu rike da mukaman siyasa da ake sa ido a kansu. Thenation ta rahoto.
Hukumar ta sake caccakar Gwamna Bello Muhammed Matawalle kan zargin karbar cin hancin dala miliyan 2 da ake alakantawa da shugabanta, Abdulrasheed Bawa.
Ya bayyana zargin a matsayin yaudara.
A cikin wata sanarwa da shugaban ta na yada labarai Mista Wilson Uwujaren ya fitar, EFCC ta bukaci abokan huldar ta na kasa da kasa da su dakile kubucewar PEPs.
Sanarwar ta ce: “Haka kuma, hukumar na son sanar da jama’a game da shirye-shiryen da wasu Yan siyasa da ake zargi da cin hanci da rashawa ke yi na ficewa daga kasar nan gabanin ranar 29 ga watan Mayu.
"Hukumar tana aiki tare da hadin gwiwa tare da takwarorinta na kasa da kasa don dakile wadannan tsare-tsaren tserewa tare da gurfanar da wadanda ke zargi a gaban kotun shari'a."
BY isyaku.com
RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI