Hukumar Kwastam ta Najeriya reshen jihar Kebbi, ta samu nasarar kwace kayakin laifi guda 17 tsakanin 15 ga Afrilu zuwa 15 ga Mayu 2023.
Kwanturolan Hukumar Kwastam na Jihar Kebbi Dr. Ben Oramalugo ne ya bayyana hakan a yayin ganawa da manema labarai a hedikwatar rundunar a Birnin kebbi a ranar Juma’a 19 ga Mayu 2023. Kafar yada labarai na yanar gizo isyaku.com ya rahoto.
Kwanturolan ya ce rundunar ta kama wata mota makare da naman Jaki da fata a kan hanyar Bunza - Kanba a lokacin da ake bincike bayan samun rahoton sirri.
Kwanturolan ya ce:
“A yayin da jami'an rundunar suke binciken motar bayan sun kama ta, wasu batagari daga kauyen Bunza da ke karamar hukumar Bunza ta jihar Kebbi sun far wa jami’an".
"Daga baya mun yi kira soji domin agaza mana, kafin isowar sojojin, gungun batqgarin sun yi nasarar jaye motar zuwa daji dake yankin."
"Jami'an mu da sojoji sun yi hakuri har zuwa sa'o'i kadan kafin su ci gaba da gudanar da ayyukansu, motar da abin da ke ciki an gano ta ne da misalin karfe 0100 na safe a wani waje daban kuma yanzu haka an kawo motar hedikwatar Kwastam a Birnin kebbi." Yace.
Abubuwan da aka kwace sun hada da:
1. Motar Volvo guda daya (tayoyi 6) cike take da manyan buhu 212 da kananan buhuna 202 na naman jaki.
2. Motoci 4 da aka yi amfani da su da suka hada da Toyota Camry 2013 guda 2, da wasu motoci 2 da aka yi amfani da su har da Honda Jazz 2005.
3. Dilan kayakin sawa "Gwanjo" guda 55.
4. Litar man fetur 4,925
5. Buhunan shinkafa 13 na kasar waje.
6. Jarkoki 5 na mangyada.
7. Volvo 1 launin shudi (tayoyi 6) da Toyota Corolla ruwan toka guda É—aya azaman hanyar isar da sako da sauransu.
Adadin kudin harajin na kayayyakin da aka kama ya kai miliyan saba'in da daya, dubu dari biyu da tamanin da bakwai, Naira hamsin da shida (N71,287,056).
Dokta Oramalugo ya ce rundunar a cikin watan Afrilu ta samu kudaden shiga miliyan dari da ashirin da bakwai, da dubu dari uku da sittin da hudu, da naira dari daya kacal (N127,364,100).
Kwanturolan ya alakanta wannan nasarar ga jiga-jigan zaratan jami’an rundunar hada da dukkanin sassan rundunar tare da mai da hankali kan sashin leken asiri na kwastam, da kuma kokarin wasu jami’ai da suka yi ritaya, shugabannin al’umma da wadanda suka taimaka da shawarwari masu kyau wanda ya kai ga nasarar da aka samu.
BY isyaku.com