Type Here to Get Search Results !

Gwamnatin jihar Kano ta kalubalanci yan sanda su kawo mata hujja kan tuhumar kisan kai da suke yi wa Alhassan Ado Doguwa


Gwamnatin jihar Kano ta bukaci ‘yan sanda da su kawo mata cikakkun bayanai kan zargin kisan kai da ake yi wa dan majalisar wakilai, Alhassan Ado Doguwa, idan har za ta gurfanar da shugaban masu rinjaye na majalisar dokokin kasar.

 An tattaro cewa Kwamishinan ‘yan sanda na Kano ya mika rahoton zargin kisan kai da sauran laifuka ga ma’aikatar shari’a ta jihar Kano a ranar Juma’a domin duba yiwuwar daukar mataki na gaba. The nation ta rahoto.

 Sai dai ma’aikatar shari’a ta jihar ta mayar da takardun karar hannun ‘yan sanda domin ta binciki lamarin sosai tare da bayar da cikakken bayani kan zargin da ake yi wa Doguwa.

 Babban Lauyan Jihar Kano kuma Kwamishinan Shari’a na Jihar Kano, Musa Abdullahi Lawan, a ranar Juma’a ya shaida wa manema labarai cewa ma’aikatar ta bukaci (’yan sanda) da su bayar da gamsassun hujjoji irin hotunan gawa, bayanan shaidu, bindigar da aka kwato da sauran kayayyaki da dama, don tabbatar da laifukan da ake tuhuma.

Post a Comment

0 Comments
* Please Don't Spam Here. All the Comments are Reviewed by Admin.

Top Post Ad

Below Post Ad

Shiga group dinmu na WhatsApp domin samun labaran mu kai tsaye LATSA NAN
Domin zama Wakilin mu a garin ku LATSA NAN
Domin aiko Sako/Labari/Korafi LATSA NAN
Domin samun labaran mu a Facebook LATSA NAN
Domin samun labaranmu a Twitter LATSA NAN