Ta fara kwabewa: 'Ƴan bindiga na yin hijira daga Zamfara zuwa Kaduna don neman mafaka'


Mazauna ƙauyukan Kaduna sun nuna damuwarsu tare da ankarar da cewa 'yan bindiga da ke tsere wa luguden wutar da ake musu a Zamfara na samun mafaka a dazukan da ke kusa da su. BBC ya wallafa.

Garuruwan da ke iyaka tsakanin Zamfara da Kaduna ne suka fitar da wannan korafi, tare da cewa suna ganin 'yan bindiga na yi musu shawagi.

Mazauna kauyen Damari a karamar hukumar Birnin Gwari sun ce 'yan bindiga na shigar garuruwansu da tsakar rana.

Jaridar Daily Trust ta Najeriya da ta wallafa labarin, ta kuma rawaito wani Saeed Damari da ke cewa tun ranar Talata 'yan bindiga ke kwarara zuwa cikin dajin Kuduru.

Haka zalika shi ma wani mazaunin yankin ya shaida cewa 'yan bindigar na yi musu barazanar garkuwa da manoma.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN