Rundunar ‘yan sanda a babban birnin tarayya Abuja ta kama wani yaro dan shekara 16 mai suna Emmanuel John da laifin dukan mahaifinsa, Monday John, har lahira. Shafin labarai na isyaku.com ya samo.
Majiyoyin ‘yan sanda sun ce Emmanuel ya kwada wa mahaifinsa Tabarya a lokacin da suke fada da mahaifiyarsa, Mercy John, a gidansu a ranar 2 ga watan Mayu da misalin karfe 10 na dare.
An ce ma’auratan sun yi zazzafar cece-kuce wanda ya rikide zuwa fada. Emmanuel ya goyi bayan mahaifiyarsa ya kai wa mahaifinsa duka.
A lokacin da yake fada da babansa, sai ya dauko Tqbarya ya kwada wa mahaifinsa. Mahaifin ya fadi, aka garzaya da shi asibiti inda aka tabbatar da rasuwarsa.
Rundunar ‘yan sandan ta ce wani Yusuf Ayuba ne ya kai kara a ofishin ‘yan sanda na Karshi ranar Laraba, 3 ga watan Mayu.
An kama wanda ake zargin kuma za a gurfanar da shi a gaban kotun matasa idan an kammala bincike.
BY ISYAKU.COM
RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI