Martabar Sarakunan jihar Kebbi ya dawo, farin ciki ya bayyana

Martabar Sarakunan jihar Kebbi ya dawo, farin ciki ya bayyana


Masu Martaba Sarakunan Argungu, Gwandu, Yauri da Zuru a jihar Kebbi sun dara bayan Gwamnan jihar Kebbi Nasir Idris ya yi alkawarin ci gaba da Martaba tare da mutunta su a Gwamnatinsa.

A wajen taron rantsar da Nasir Idris a matsayin Gwamna a filin wasa na Hiliru Abdu a garin Birnin kebbi ranar Litinin 29 ga watan Mayu 2023, kafar labarai na isyaku.com ya lura Sarakunan na cike da farin ciki wanda ya bayyana a zahiri a fuskokinsu.

Wani mai jawabi a wajen taro Malam Isyaka Easy ya ce Gwamnatin jihar Kebbi karkashin shugabacin Nasir Idris za ta Martaba Sarakuna kuma za a yi tafiya tare da su a matsayinsu na ubannin al'umma.

A baya dai, wani tsohon Minista Alhaji Saidu Samaila Sambawa, a wani faifen bidiyo gabanin zabukan 2023, ya zargi tsohon Gwamnan jihar Kebbi Abubakar Atiku Bagudu da kin ji, balle karbar shawarwari don gyara tafiyar mukin jihar Kebbi ciki har da zargin rashin mutunta Sarakunan jihar Kebbi a karkashin mulkinsa. 

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN