Lauyan jam’iyyar All Progressives Congress (APC), Adeniyi Akintola (SAN), ya sanar da kotun sauraron kararrakin zaben shugaban kasa cewa babu wani lauya a cikin tawagarsu da ya isa ya yi magana da manema labarai kan ci gaba da shari’ar.
Akintola yana mayar da martani ne ga shawarar da alkalin kotun, Mai shari’a Haruna Tsammani ya ba wa daukacin wadanda suka shigar da kara na su rage yawan lauyoyin da ke tawagarsu domin a ba jama’a dama.
Da yake mayar da martani, Akintola ya ce, sun hana lauyoyin da ke cikin tawagarsu damar ba ‘yan jarida taron manema labarai da aka saba yi, inda ya ce duk lauyan da ya yi hakan za a kori shi daga kungiyar.
Ya ce: “Ya shugabana, idan ka lura babu wani daga cikin lauyoyinmu da ya yi haka, duk abin da aka faɗa a nan ya kare a nan,” in ji shi.
Ya kuma shaida wa kotun cewa tawagarsu ta kunshi manyan lauyoyi 38 na Najeriya da wasu lauyoyi an yi musu kwaskwarima kuma kowane lauya ya san makon da za su halarci zaman.
Tun da farko, babban lauyan jam’iyyar PDP da Atiku Abubakar, Chris Uche (SAN), ya tabbatar wa kotun cewa tawagar lauyoyin za ta yi wa tawaga ta lauyoyin su kwaskwarima bisa bukatar hakan.
Ya ce, duk da haka, ya ce lokacin gabatar da kararrakin zabe na ba lauyoyi damar da za su iya koyan yadda ake gudanar da zaben.
BY isyaku.com
RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI