Type Here to Get Search Results !

Main event

Kotun Koli ta kori karar PDP kan takarar Tinubu da Shettima


Kotun Koli ta yi watsa da karar da Jam’iyyyar PDP ta shigar na neman kotun soke takarar Bola Bola Tinubu da Kashim Shettima a matsayin dan takarar Shugaban kasa da mataimakinsa a Jam’iyyar APC zaben 2023 da ya gabata.

Kotun ta yi fatali da karar da cewa babbar jam’iyyar adawar ba ta da hurumin tsoma baki a cikin harkokin cikin gida na jam’iyyar APC, wadda sha’anin cikin gidanta ne tsayar da ’yan takararta. Jaridar Aminiya ta rahoto.

Alkaln kotun su biyar sun yanke hukuncin ne a safiyar Juma’a, kwana biyu kafin ranar rantsar da Tinubu da Shettima a ranar Litinin.

A ranar Alhamis aka kaddamar da bukukuwan mika musu mulki, inda shugaba Buhari ya mika wa Tinubu kundin bayanan ayyukan gwamnati, sannan ya karrama shi da lambar girmamawa ta kasa mafi daraja ta GCFR, wadda ake ba wa shugabannin kasa.

An kuma karrama Shettima da lambar da GCON, wadda ke biye da GCFR, a matsayin matamakin shugaban kasa mai jiran gado.

Post a Comment

0 Comments
* Please Don't Spam Here. All the Comments are Reviewed by Admin.

Top Post Ad

Below Post Ad

Shiga group dinmu na WhatsApp domin samun labaran mu kai tsaye LATSA NAN
Domin zama Wakilin mu a garin ku LATSA NAN
Domin aiko Sako/Labari/Korafi LATSA NAN
Domin samun labaran mu a Facebook LATSA NAN
Domin samun labaranmu a Twitter LATSA NAN

Hollywood Movies