A gabanin litinin 29 ga watan Mayu, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya jagoranci magajinsa, Bola Ahmed Tinubu ya zagaya da shi fadar shugaban kasa ta Aso rock villa, a Abuja.
Ana sa ran zababben shugaban zai koma cikin Villa, ofishi da gidan shugaban Najeriya bayan rantsar da shi a ranar Litinin mai zuwa.
Ziyarar da shugaban kasa da zababben shugaban kasa suka kai a fadar shugaban kasa ya gudana ne bayan da shugabannin biyu suka yi sallar Juma'a tare a masallacin fadar shugaban kasa.
Ga karin hotunan rangadin da Sunday Aghaeze ya dauka a kasa.
BY isyaku.com
RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI