Wani dan sandan Najeriya, Anas Bello Bungundu da matarsa, Hassana Musa Yusuf, sun mutu a wani hatsarin mota.
An tattaro cewa hatsarin ya afku ne a ranar Juma’a, 5 ga Mayu, 2023, a jihar Sokoto.
Nan take matarsa ta rasu yayin da aka garzaya da Anas zuwa UDUTH, Sokoto, inda ya rasu a ranar Talata 9 ga watan Mayu.
Ma'auratan sun yi aure a bara.
Wani abokin aikinsa, ASP Isah Lukman Imam, wanda ya tabbatar da wannan labari mai ban tausayi a wani sako da ya wallafa a Facebook a ranar Laraba, 10 ga watan Mayu, ya ce ma’auratan na kan hanyarsu ta zuwa daurin auren abokinsu ne a lokacin da hatsarin ya afku.
BY ISYAKU.COM