![]() |
Illustrative picture |
Iyayen daliban da aka sace na Kwalejin Gwamnatin Tarayya (FGC) da ke Birnin Yauri da ke jihar Kebbi, sun bayyana kwarin guiwar ganin an sako sauran daliban biyu da har yanzu ake tsare da su.
Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) ya ruwaito cewa ‘yan bindiga karkashin Dogo Gide sun yi garkuwa da dalibai da malaman kwalejin sama da 96 a ranar 17 ga watan Yuni, 2021.
Ya zuwa yanzu dai an kubutar da duk wadanda aka sace in ban da guda biyu.
Daya daga cikin iyayen, Saddiq Ka’oje ya ce sai sun kafa kungiya domin tattaunawa da ‘yan bindigar kai tsaye.
“Wannan yana haifar da sakamako mai amfani. Da farko dai sauran daliban da aka yi garkuwa da su 11 ne amma da wannan tattaunawa mun sami nasarar ceto hudu a farkon lamarin.
“‘Daga baya, an kuma ceto dalibai guda biyu, kuma a ranar jiya mun sake ceto wasu uku.
“Muna ba da daukaka ga Mahaliccinmu, yanzu daga cikin dalibai 11 da suka rage, tara sun samu ‘yancinsu, kuma biyu ne kawai ake tsare da su.
"Ana ci gaba da kokarin 'yantar da su, nan ba da jimawa ba za a 'yantar da su," in ji shi.
Sai dai Ka’oje ya ki cewa komai kan kudin fansa da aka biya, amma ya yabawa gwamnatin jihar kan rawar da ta taka wajen sako daliban da aka sace.
Ya kara da cewa "Nasarar da muka samu a yau ta samu ne sakamakon kwarin gwiwa, goyon baya da kuma kokarin gwamnatin Kebbi, muna matukar godiya da abin da suka yi wajen ganin an sako wadannan rayukan da ba su ji ba ba su gani ba."
BY ISYAKU.COM
RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI