Yakubu Shehu ma’aikacin baitul mali na jihar Bauchi dake aiki a ofishin shugaban ma’aikatan jihar Bauchi (HOCS) da ‘ya’yansa biyu sun mutu a wani hatsarin mota da ya rutsa da su.
Hadarin ya afku ne a kan titin Azare/Sakwaa a karamar hukumar Zaki ta jihar Bauchi da yammacin ranar Asabar, 13 ga watan Mayu, 2023.
Wata majiya a garin Azare ta shaida wa jaridar Nigerian Tribune cewa marigayi Yakubu da ‘ya’yansa biyu sun mutu nan take bayan hadarin.
Majiyar ta ce Yakubu na zuwa kauyensu ne domin halartar daurin auren dangi tare da ’ya’yansa, sai motarsa ta kauce daga kan hanya, biyo bayan fashewar tayar motar, sakamakon haka motar ta ci karo da wata katuwar bishiya da ke gefen titin.
Ya kara da cewa motar ta kusan tsagewa gida biyu sakamakon hadarin.
An yi jana’izar mahaifin da ‘ya’yansu da rana kamar yadda addinin Musulunci ya tanada a garin Sakwa da ke kauyensu.
Daga cikin wadanda suka halarci sallar jana’izar akwai wakilin shugaban ma’aikatan jihar Bauchi, da sakatarorin dindindin guda biyu, da Daraktoci uku na ofishin.
BY isyaku.com