Rundunar 'yan sanda ta kwace babbar Sakatariyar jam'iyyar Labour Party reshen jihar Imo da ke kudu maso gabashin Najeriya. Legit ya wallafa.
Sakataren LP na ƙasa, Umar Farouk, ne ya tabbatar da faruwar lamarin a wata sanarwa da ya fitar ranar Litinin 3 ga watan Afrilu, 2023.
Jaridar Vanguard ta rahoto Sanarwan na cewa:
Uwar jam'iyyar LP ta ƙasa ta kaɗu na samun labarin mamaya da kuma kwace Sakatariyarta da ke Owerri, yau Litinin 3 ga watan Afrilu, 2023. Hakan ya biyo bayan wanda ya faru ranar Laraba 15 ga watan Maris."
Sakataren LP ya kara da cewa gwamnatin Imo ta jam'iyyar APC ta ce an É—auki wannan matakin ne saboda cika umarnin Kotu.
BY ISYAKU.COM
RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI