Shahararren mawakin Najeriya David “Davido” Adeleke ya bayyana cewa attajirin da ya fi kowa kudi a Afirka, Alhaji Aliko Dangote ya taimaka masa wajen halayen neman kudi.
Ya bayyana hakan ne a wata hira da Forbes ta yi a baya bayan nan yayin da yake Botswana don halartar taron Forbes 30 Under 30. PM News ta rahoto.
Randall Lane, Babban Jami’in Kula da Abubuwan Cikin Gida na Forbes (CCO), ya tambayi Davido, wanda ya shahara da son motoci masu tsada da kuma salon rayuwar almubazzaranci, game da dangantakarsa da Dangote.
Da yake mayar da martani, Davido ya tabbatar da cewa mahaifinsa hamshakin attajirin nan, Cif Adedeji Adeleke, aminin Dangote ne. Ya kuma bayyana cewa kullum Dangote yana ba shi shawarar ya ajiye kudinsa ko kuma ya zuba jari.
Kalamansa, “Uncle Aliko [Dangote] wani hamshakin attajiri ne na daban. Kawu Aliko yana saye kamar motoci biyu duk shekara takwas. Shi É—an biloniya ne mai tarbiya kuma daban-daban.
"Duk lokacin da na gan shi, sai kawai ya ce abu ɗaya, 'Ajiye kuɗin ka!'. Babu wani abu da ya ƙara gaya mani, duk lokacin da ka ajiye kuɗin ka. Shi da babana sun kasance abokai na kud da kud.
“Kuma shi (Dangote) ya yi mana kyau (’yan Najeriya) a gida. Ya samar da masana'antu da yawa. Ya bude babbar masana'anta a Afirka. Wannan yana ba da aikin yi. "
Tare da kimanin dala biliyan 20.5, Dangote ya kasance mutumin da ya fi kowa arziki a Afirka, baƙar fata mafi arziki a duniya, kuma na 83 a duniya mafi arziki, a cewar Bloomberg Billionaires Index.
BY ISYAKU.COM
RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI