Rahotanni daga garin Birnin kebbi a jihar Kebbi na cewa ana zargin jami'an soji sun yi wa jama'a duka a ofishin KEDCO da ke GRA Nepa a garin Birnin kebbi. Shafin labarai na isyaku.com ya samo.
Lamarin ya faru ne da misalin karfe 1:30 na ranar Asabar 29 ga watan Afrilu. Gaddafi Ibrahim, Manajan KEDCO na jihar Kebbi, a wani faifen bidiyo, ya ce jami'an sun shigo harabar KEDCO inda suka yi wa wasu bayin Allah duka
Ya ce wadanda lamarin ya shafa sun hada da shi kansa inda ya sami targade a hannu, sai kuma jami'an tsaro Black Tiger Security da ke tsaron harabar maaikatar duk an yi masu duka.
Ya kara da cewa lamarin ya rutsa da kwastomomi da suka je KEDCO don su biya kudin wuta, cikinsu har da wani Alakali.
Ba wani tabbaci, ko bayani da shafin labarai na yanar gizo isyaku.com ya samu daga barikin soji na Birnin kebbi kan lamarin. Kazalika wata majiya ta bukaci wakilin isyaku.com ya tuntubi ofishin soji ranar Litinin don tantance zargin.
BY ISYAKU.COM