Gwamnan jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya ce gwamnatinsa ta shirya tsaf domin miƙa mulki ga sabuwar gwamnatin cikin ruwan sanyi ba tare da hayaniya ba. Legit ya wallafa.
Gwamnan ya faÉ—i haka ne a wata sanarwa da kwamishinan yaÉ—a labarai da harkokin cikin gida, Muhammad Garba, ya fitar, kamar yadda Channels tv ta rahoto.
Ya kuma musanta zargin da jam'iyyar NNPP ta yi cewa gwamnati mai barin gado na kulla makirci da zagon ƙasa a shrin miƙa mulki ga zababben gwamna, Abba Ƙabir Yusuf.
Kwamishinan ya ƙara da cewa tuni kwamitin miƙa mulki da sauran kananan kwamitoci a ma'aikatu da hukumomi suka maida hankali wajen shirin miƙa mulki lami lafiya.
Ya kuma yi bayanin cewa sun sanya wakilan sabuwar gwamnati a cikin kwamitin miƙa mulki ne domin tabbatar da gaskiya da yin komai a buɗe.
A ruwayar Vanguard, Garba ya ce:
"Manufar kafa kwamitim miƙa mulki shi ne ya shirya duk abinda ya kamata ya miƙa bayanai daga gwamnati mai barin gado zuwa sabuwar gwamnati ba tare nuna aƙida ba."
Ya yi kira ga wasu tsirarun mutane daga bangaren gwamnati mai zuwa da su san nauyin dake kansu, su maida hankali wurin tabbatar da an rabu cikin ruwan sanyi.
Bugu da ƙari, kwamishinan ya ce gwamnati mai barin gado ta yi tsammanin irin waɗannan akidoji da sabbin tsare-tsare daga NNPP amma duk saurin unguwar zoma ta bari a haihu, su bari a rantsar da sabuwar gwamnati.
BY ISYAKU.COM