Illustrative picture only |
Hukumar kula da harkokin shari’a ta jihar Jigawa ta umurci alkalin babbar kotun shari’a, ya je hutun ritayar dole bisa zarginsa da aikata ba daidai ba.
Hukumar ta kuma nada wasu manyan ma’aikatan hukumar su hudu, a mukamai daban-daban.
Sanarwar hakan ta samu sa hannun daraktan yada labarai da ka’idojin shari’a na jihar Mista Abbas Rufa’i a ranar Asabar.
Sanarwar ta ce, an yanke wannan shawarar ne a yayin taro karo na 170 na hukumar kula da harkokin shari’a ta jihar da aka gudanar a Dutse, jihar Jigawa a ranar Alhamis.
“Hukumar ta yanke shawarar yin ritayar dole wa Alkali Safiyanu Muhammad’ bisa zargin aikata laifin a lokacin da wani mai kara ya gurfana a gabansa a wata Kotun Shari’a ta Upper Shari’a da ke Birnin Kudu.
Sai dai hukumar ta gargadi ma’aikatan ta da su guji duk wani nau’i na cin hanci da rashawa, domin tsaftace bangaren shari’a a jihar.
Don haka ta kara da cewa hukumar ta sake jaddada aniyar ta na tunkarar duk wani ma’aikaci da ke aikata ba dai-dai ba.
Bugu da kari, hukumar ta yanke shawarar nada Mista Aliyu Muhammed a matsayin mataimakin babban magatakarda na biyu na kotun daukaka kara ta Shari’a da kuma Abdulrashid Alhassan a matsayin babban sufeto, kotun daukaka kara ta Shari’a.
Sauran sun hada da Muhammad Lawan a matsayin mataimakin babban sufeto na shiyyar, kotun daukaka kara ta shari’a da Muhammad Adamu mataimakin babban sufeto na shiyyar, kotun daukaka kara ta shari’a.
A halin da ake ciki, bisa ga dokar da ta kafa hukumar da aikinta, kungiyar alkalan kotunan shari’a ta jihar Jigawa (JISSJA), ta yabawa hukumar bisa wannan nasara da ta samu tare da ba kungiyar tabbacin goyon bayansu da hadin kai.
BY ISYAKU.COM