Type Here to Get Search Results !

Main event

Daga karshe an zartar da hukuncin Kotu kan zakaran da ya dami makwabta


Mutumin da ya mallaki zakaran da aka zartar wa hukuncin kisa a jihar Kano, ya ce bai ji daɗin yadda marigayin ya haɗa shi faɗa da maƙwabcinsa ba.

A ranar Talatar da ta gabata ne, Mai shari’a Halima Wali a wata kotu da ke Kano ta yanke wa zakaran hukuncin kisa. BBC ya wallafa.

Matakin ya zo ne bayan wasu maƙwabtan mai zakaran biyu suka shigar da ƙara, inda suka zargi zakaran da hana su sakat saboda yawan cara, da zarar sanyin asuba ya kaɗa.

A tattaunawarsa da BBC, mai zakaran, Isiyaku Shu’aibu, mazaunin unguwar Ja’en a birnin Kano, ya ce bai taÉ“a samun saÉ“ani da makwabcinsa ba a tsawon shekara 20 sai a dalilin zakaran.

Ya kuma ce ba zai yi kewar zakaran ba, kasancewar ba wata shaƙuwar ƙut-da-ƙut suka yi ba.

Isyaku ya shaida wa BBC cewa yara ne ma suka yanka rigimammen zakaran kafin ma ya dawo gida a ranar Juma’a.

Tun farko, ɗaya daga cikin waɗanda suka shigar da ƙarar, Yusuf Muhammad, ya ce carar da zakaran ke yi, tana shiga haƙƙinsa don kuwa ba ya samun barci cikin lumana.

Isyaku Shu’aibu ya faÉ—a wa kotun cewa da ma ya sayi zakaran ne don bikin Easter, inda ya buÆ™aci kotun ta yi masa rangwame zuwa ranar Juma’a kafin zartas masa da hukunci don amfani da naman a ranar Good Friday, abin da kotun ta amince da shi.


Post a Comment

0 Comments
* Please Don't Spam Here. All the Comments are Reviewed by Admin.

Top Post Ad

Below Post Ad

Shiga group dinmu na WhatsApp domin samun labaran mu kai tsaye LATSA NAN
Domin zama Wakilin mu a garin ku LATSA NAN
Domin aiko Sako/Labari/Korafi LATSA NAN
Domin samun labaran mu a Facebook LATSA NAN
Domin samun labaranmu a Twitter LATSA NAN

Hollywood Movies