Tahajjud: An haramtawa Limamai karanta Qur'ani ta waya a sallolin watan Ramadana


An haramtawa limaman masallatai a kasar Kuwait rike wayoyin hannu suna karanta Al-Qur’ani yayin da suke jan nafila a dararen watan, rahoton BBC.

Wannan na zuwa ne daga ma’aikatar wakafi da harkokin addini Islama na kasar yayin da ake tunkarar dararen 10 na karshe a watan mai alfarma.

Rahoto ya bayyana cewa, Salah Al Shilahi, karaminin ministan kula da harkokin masallatai na kasar ne ya fitar sanarwar.

Ministan ya yi wannan bayanin tare da bayyana fa’idojin da wannan dokar za ta kawo ga al’umma da kuma su kansu limaman.

Dalilin sanya wannan dokar hana karanta Al-Qur’ani ta waya

A cewar sanarwar ministan, hanin zai amfani limamai sosai, kasancewar hakan zai iya taimaka musu wajen gyaran haddarsu ta littafin mai tsarki, Gulf News ta ruwaito.

Hakazalika, ya ce dokar wata hanya ce ta karfafawa sauran al’umma gwiwa wajen riko da haddar Al-Qur’ani a madadin neman wasu hanyoyi.

A bangare guda, ministan ya nemi dukkan limamai su yi muraji’a haddarsu yadda ya kamata kafin shiga gaban masallaci don jan sallar Tarawih ko Tahajjudi.

Ba wannan ne karon farko da ake sanya dokoki game da ibada ba a duniya, an sha yin hakan a wurare daban-daban, musannan kasashen Musulmai masu riko da addinin da kuma hukumomin da ke kula da harkokin addini.

Hukumomin Saudiyya sun bayyana cewa, ya kamata Musulmai su zama masu mutunta maslalatan harami guda biyu a lokacin da suka kai ziyarar ibada a kasar.

Ba sabon abu bane ganin jama’a suna yawan yada hotunan da suka dauka a lokutan ibadan Hajji ko Umrah ba a kasar ta Saudiyya.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN