J
am'iyyar All Progressives Congress (APC) ta ce da zaran zaɓaɓɓen shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya dawo Najeriya daga Turai zai ɗora aiki daga inda ya tsaya.
am'iyyar All Progressives Congress (APC) ta ce da zaran zaɓaɓɓen shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya dawo Najeriya daga Turai zai ɗora aiki daga inda ya tsaya.
Haka nan kuma Jam'iyyar ta ce shugaban ƙasa mai jiran gado, wanda ya sa kafa ya bar Najeriya tun ranar 22 ga watan Maris, zai dawo nan ba da jimawa ba gabanin ranar 29 ga watan Mayu, 2023. Legit ya wallafa.
Sakataren yaɗa labarai na APC ta ƙasa, Felix Morka ne ya yi wannan furucin a cikin shirin Politics Today na Channels tv ranar Alhamis, 13 ga watan Afrilu, 2023.
Yayin da aka tambaye shi ko ina zaɓabben shugaban ƙasan ya shiga yanzu haka, Kakakin APC ya bayyana cewa:
"Yana nan lafiya kalau, bayan kammala zaɓe da duk faɗi tashin da aka yi na gajiya, ya yanke shawarin ya ɗan tafi ya sarara, ya samu hutu."
"Da zaran ya dawo gida Najeriya kuma aka rantsar da shi ranar 29 ga watan Mayu, 2023, babu sauran zama, nauye-nauye zasu hau kansa na jan ragamar ƙasa mai girma kuma mai ɓangarori kamar Najeriya."
"Na san cewa nan ba da jimawa ba (shugaban ƙasa mai jiram gado) zai dawo gida Najeriya."
Mista Morka ya ƙara da bayanin cewa tsohon gwamnan Legas ɗin ba zai samu hutu yanda ya dace ba idan ya zauna a Najeriya bayan zaɓe, mutane zasu dame shi don neman muƙami.
Kakakin APC ya ce duk waÉ—anda ya zama wajibi suna gana wa da Tinubu ta fasahar zamani ko fuska da fuska kuma ya kamata kowa ya sani yana aiki kan abinda ke tunkarowa.
BY ISYAKU.COM