A cewar jaridar Punch, lamarin ya faru ne da misalin karfe 1:30 na ranar Laraba, 12 ga Afrilu, 2023.
Wata majiya ta ce dalibar ta karbo rigarta ta bikin kammala karatunta ne domin bikin da aka shirya yi ranar Alhamis 13 ga watan Afrilu, sannan ta koma aji a lokacin da lamarin ya faru.
Wani babban ma’aikacin makarantar ya shaida wa jaridar cewa an garzaya da marigayiya Aminat asibitin makarantar ne bayan ta yanke jiki ta fadi.
Daga baya aka kai ta makabartar Musulmi, wato Osere, don yin Janaza da binne ta.
Yayin da yake magana a wajen binne ta, an jiyo mahaifin marigayiyar ya ce “ba ta nuna wata alamar damuwa ko wata alama ta rashin lafiya ba. Mun yi doguwar tattaunawa kan batutuwa da dama kafin in raka ta don ta samu taksi zuwa makarantar.
Jami’ar hulda da jama’a ta kwalejin, Mrs Abibat Zubair, wadda ta tabbatar da faruwar lamarin, ta ce marigayiyar dalibar Music/Yoruba ce, inda ta kara da cewa kwalejin da daliban sun yi jimamin mutuwarta a yayin bikin karramawar.
"Provost ya ziyarci iyayenta jiya don jajanta musu, ya kuma yi makokinta a yau yayin bikin karramawar tare da daliban kwalejin," in ji PRO .
BY ISYAKU.COM
RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI