An tsinci jarirai biyu da ransu bayan an haife su kuma aka yar da su a wurare daban daban a jihar Kebbi.
Lamarin ya faru ne a mako na farko.kafin shigowar watan Ramadana. Shafin labarai na yanar gizo isyaku.com ya ruwaito
Kwamandan Hisbah na jihar Kebbi Ustaz Sulaiman Muhammad ya sanar wa manema lamarai ranar Talata 25 ga watan Afrilu 2023 a garin Birnin kebbi.
Ya ce an tsinci jariri na farko an yar da shi a bola a Unguwar Badariya a garin Birnin kebbi.
Yayin da aka tsinci jariri na biyu a garin Ambursa. Ya ce duk jariran na raye lokacin da aka tsincesu, kuma ana kula da su a gidan Marayu a garin Birnin kebbi.
BY ISYAKU.COM