Yanzu-Yanzu: Dalibai 'Yan Najeriya Sun Shiga Tsaka Mai Wuya Kan Hanyar Su Ta Dawowa Daga Sudan


Wasu daga cikin ɗalibai ƴan Najeriya da aka kwaso daga rikicin Sudan, yanzu haka sun maƙale a cikin tsakiyar hamada, rahoton Daily Trust ya tabbatar.

Bayan tsagaita wuta da ɓangarorin da ke faɗa da juna suka sanar na kwana uku, ƙasashe da dama sun matsa ƙaimi domin kwashe ƴan ƙasar su daga Sudan.

A ranar Laraba, gwamnatin tarayya ta bayyana cewa ta fitar da N150m domin ɗaukar hayar manyan motoci 40, da za su kwaso wasu ƴan Najeriya daga Sudan zuwa birnin Alkhahira na ƙasar Masar, inda daga nan za a kwaso su a jirgi zuwa Najeriya.

Sai dai wasu daga cikin ɗaliban da aka kwaso domin kai su wajen tsiria, sun bayyana halin ƙuncin da suke ciki a tafiyar.

Wata ɗaliba wacce lamarin ya ritsa da ita wacce ba ta ambaci sunan ta ba, tace direbobin sun sha alwashin ƙin cigaba da tafiyar saboda ba a biya su kuɗin su ba.

A kalamanta:

"Kafin mu fara wannan tafiyar, mun ga abubuwa iri-iri. Saboda Allah mun kwashe sama da sa'o'i biyar muna cikin hamada. Ba mu san halin ma da mu ke ciki ba a yanzu."

"Ba mu da ruwa. Kuɗaɗen mu sun ƙare. Direbobin sun ce ba za su tafi da motocin su ba tunda ba a biya su kuɗin su ba. Ga mu nan maƙale a cikin hamada. Ba mu da komai. Ba ma mu san a inda mu ke ba. Muna cikin wajen da ba mu san ko ina ne ba sannan cikin babban haɗari."

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN