Daniel Bwala wanda Mai magana da yawun bakin Atiku Abubakar ne a zaben 2023, ya yi hasashen yadda Gwamnatin mai zuwa za ta kasance.
A ranar Juma’a, Daniel Bwala ya rika jero wasu ‘yan siyasa da kuma mukaman da yake ganin za su samu idan Bola Ahmed Tinubu ya hau karagar mulki. Legit ya wallafa.
Tsohon jagoran na jam’iyyar APC mai mulki ya yi hasashen wadanda za su zama Ministoci, Hadiman shugaban Najeriya da kuma shugabannin majalisa.
Kamar yadda Vanguard ta bibiyi ‘dan siyasar a shafinsa, ga yadda ya yi hasashen na shi:
Jerin shugabannin gobe
Shugaban kasa - Bola Ahmed Tinubu
Mataimakin shugaban kasa - Kashim Shetima
Shugaban majalisar dattawa - Godswill Akpabio
Shugaban ma’aikatan fada - Femi Gbajabiamila
Mai bada shawara kan tsaro - Nuhu Ribadu
Hadimin harkar cikin gida - Babajimi Benson
Sakataren gwamnatin kasa - Nasir El-Rufai
Mai magana da yawu - Festus Kayamo
Ministan harkar musamman - James Faleke
Ministan birinin Abuja - Yahaya Bello
Ministan tsaro - Tukur Buratai
Ministan yada labarai - Bayo Ononuga
Ministan harkokin waje - Kayode Fayemi
Ministan cikin gida - Nyesom Wike
Ministan shari’a (AGF) - Babatunde Fashola
Ministan harkar noma - Ben Ayade
Ministan jiragen sama - Femi Fani Kayode
Ministan ayyuka - Ken Nnamani
Lauyan gidan gwamnati - Babatunde Ogala
Rahoton Daily Post ya nuna Bwala ya hango Dele Alake a kujerar Jakadan Najeriya a Amurka, amma bai san shugaban majalisar wakilai ba.
A cewarsa, Buba Marwa zai cigaba da rike NDLEA, sai Wale Edun ya zama Gwamnan babban banki, ya yi gum a kan kujerun EFCC, DSS da NIA.
BY ISYAKU.COM