Gwamnan jiha Rivers Nyesom Wike a ranar Juma'a ya kai ziyarta ga zababben shugaban kasa, Asiwaju Bola Tinubu.
Tinubu na zaune ne a wani gida da aka ware masa gabanin rantsar da shi a matsayin shugaban Najeriya ranar 29 ga Mayu, 2023. PM News ya rahoto.
Kalli bidiyo a kasa:
Wike ya dira Abuja a ziyarar tare da takwaransa na jihar Oyo, Seyi Makinde.
Ya yi kira da a marawa Tinubu baya domin ganin gwamnatinsa ta samu nasara.
A cewarsa an yi zabe kuma ya yi nasara, yana mai cewa ya zama wajibi dukkan ‘yan Najeriya su ba shi goyon bayan da ya dace domin amfanin ‘yan Najeriya.
Gwamnan ya ce lokacin siyasa ya wuce, ya kara da cewa yana da yakinin cewa Tinubu na da abin da ya kamata ya yi wa Najeriya.
Wike ya yi aiki tukuru don fitowar Tinubu a matsayin zababben shugaban kasa yayin da ya kai masa kuri’un Rivers.
Haka kuma, Makinde ya tabbatar da cewa Tinubu ya yi nasara sosai a jihar Oyo yayin zaben shugaban kasa da aka gudanar a ranar 25 ga watan Fabrairu.
BY ISYAKU.COM
RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI