Gwamna Wike Zai Lalata Kulle-Kullen da PDP tayi wa APC a Zaben Shugaban Majalisa


Gwamna Nyesom Wike bai goyon bayan yunkurin da jam’iyyar hamayya ta PDP take yi na daura mutanenta a matsayin shugabannin majalisa.

Duk da yana ‘dan jam’iyyar PDP, The Nation ta ce Nyesom Wike yana adawa da shirin da ake yi na yakar APC a zaben shugabannin 'yan majalisar tarayya. Legit ya wallafa.

Da ‘yan jarida suka zanta da Mai girma Gwamnan a garin Fatakwal, ya nuna shirin da jam’iyyarsa take yi ba abin da zai kawo masu zaman lafiya ba ne.

Gwamna Wike ya shaidawa manema labarai ‘yan majalisan Ribas ba za su goyi baya ba.

Ana kamun kafa da Wike
A cewar Gwamnan na Ribas, duk da bai cikin ‘yan jam’iyyar APC, manyan ‘ya ‘yanta da ke neman shugabancin majalisa sun nemi ya mara masu baya

Akwai ‘yan takaran kujerar shugaban majalisar wakilan tarayya da na majalisar dattawa da suka nemi goyon bayan Gwamnan ido da ido ko ta salula

Mutane sun zo sun gana da ni. Hon. Wase (Hon. Ahmed Idris) ya zo. Sanata Godswill Akpabio ya zo. Gwamna David Umahi ya zo.
Uzor Kalu ya kira ni sau da yawa ta wayar salula daga Amurka. Me nake fada? Ba na jam’iyyarsu, damukaradiyya maganar rinjaye ce.
- Nyesom Wike

Rahoton ya kara da cewa Gwamnan ya ce ya ji ‘yan jam’iyyaradawa su na taro domin shugabancin majalisa ya fada hannunsu, ya ce ba zai yarda da wannan ba.

Wike ya bukaci ‘yan adawa da ke majalisar tarayya da su kyale jagororin jam’iyyar APC su zabi wadanda za su zama shugabanni domin wannan hakkin su ne.

Abin da Gwamnan mai barin mulki yake so shi ne APC tayi la’akari da sarkakiyar Najeriya wajen zakulo wadanda za su shugabanci majalisun tarayyar kasar.

Obi, LP v APC
Rahoto ya zo cewa Lauyan APC a kotun zabe, Thomas Ojo zai jikawa Peter Obi aiki bayan LP ta shigar da karar zaben shugaban Najeriya da aka yi a Fubrairu.

Kamar yadda Lauyan yake fada, tun farko tsohon Gwamnan na jihar Anambra ba 'Dan LP ba ne. Jam’iyya mai-ci ta na zargin Obi da saba dokar zabe na kasa.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN