Babbar magana: APC ta gaya wa Kotu NNPP bata da dan takarar Gwamna a Kano


Jam’iyyar APC ta bukaci kotu soke nasarar Abba Kabir Yusuf na Jam’iyyar NNPP a zaben Gwamnan Jihar Kano.

APC ta shaida wa Kotun Sauraron Kararrin Zaben Gwamnan Kano cewa, hasali ma, Abba Kabir, bai cancanci tsayawa takara a zaben ba. Jaridar Aminiya ta ruwaito.

Takardar karar da APC reshen Jihar Kano ta shigar ta bayyana cewa babu sunan Abba a jerin sunayen ’yan takarar da NNPP ta tura wa Hukumar Zabe ta Kasa (INEC).

Don haka ta bukaci kotun ta ayyana cewa NNPP ba ta dan takara a zaben, wanda a baya INEC ta sanar cewa Abba ne ya yi nasara.

Idan ba a manta ba, INEC ta sanar cewa Abba Kabir ya lashe zaben da kuri’u 1,019,602, a yayin da mataimakin gwamnan jihar, Nasir Yusuf Gawuna, ya zo na biyu da kuri’u 890,705.

Sai dai muna duk da cewa Gawuna ya sallama, amma APC ta shaida wa kotun cewa NNPP ba ta samu mafi rinjayen kuri’un da za a bayyana dan takararta a matsayin wanda ya yi nasara ba.

A cewarta, wasu kuri’un da aka kada wa NNPP lalatattu ne, kuma idan aka cire su, APC za ta samu rinjayen kuri’un da aka jefa.

Ta kara da cewa INEC ta tafka kuskure da ta ayyana Abba a matsayin wanda ya lashe zaben.

Bugu da kari, tazarar da ke tsakanin kuri’un Abba da Gawuna ba ta kai kuri’un da aka soke ba, don haka kamata ya yi a hukumar ta bayyana zaben a matsayin wanda bai kammala ba.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN