Da duminsa: Wani sabon maganin tari ya shigo Najeriya, NAFDAC ta yi gargadin yana kisa


Hukumar kula da ingancin abinci da magunguna a Najeriya (NAFDAC) ta gargadi ‘yan Najeriya game da wani magani mai kisa da ke yawo a kasar, NATURCOLD.

Babbar Daraktar NAFDAC, Mojisola Adeyeye ce ta bayyana gargadin a ranar Laraba, 26 ga watan Afrilun 2023, kuma ta ce rahotanni sun ce maganin ya kashe yara shida a kasar Kamaru. Legit ya wallafa.

Daraktar ta NAFDAC ta ce, maganin na tari ne, kuma babu shi a jerin magungunan da ta amince dasu wadanda aka shigo dasu daga kasashen waje, Vanguard ta ruwaito.

Ya kamata kowa ya kula, gargadin NAFDAC
Daga nan, ta ce ya kamata a kula da shigowa da kuma yawon magunguna marasa inganci, lasisi da tasiri a kasar nan, masu siya suke dubawa da kyau

Ta kuma bukaci masu shigo da magunguna, dillalai da masu saye da su guji shigowa da amfani da bogin magani a kasar.

Ta yi karin haske da cewa, magungunan bogi suna shiga Najeriya ne ta kasashen makwabta, kuma ana siyar dasu ne a kasuwar bayan fage a Najeriya.

Ku sanar da NAFDAC motsin magungunan bogi
Ta yi kira ga dillalan da ke irin wadannan magungunan da su kai su ga ofishin NAFDAC mafi kusa domin daukar mataki.

Ta ce:

“Idan kunsan wani da ya yi amfani da irin wadannan kayayyakin ko kuma ya jikkata ta dalilinsa, ana shawartar irin wannan da ya nemi taimakon gaggawa na likita daga kowane asibitin kwararru.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN