Rikicin cikin gida a jam’iyyar APC na ci gaba da habaka yayin da a karshen makon nan jam’iyyar ta kori zababben sanata David Jimkuta a karshen makon nan.
Ofishin jam’iyyar APC na karamar hukumar Takum ce ta dakatar da sabon sanatan bisa zarginsa da cin dunduniyarta. Legit ya wallafa.
Dakatar da sanatan na kunshe ne a cikin wata mudawwari mau dauke da sa hannun shugabanni 21 cikin 27 na kananan hukumomin jihar, rahoton jaridar Punch.
A cewar shugaban APC na yankin, Hon, Sirajo Sallau a cikin sanarwar mai dauke da kwanan watan 7 ga watan Afrilu, an dakatar da sanatan ne biyo bayan duba cikin tsanaki.
A cewarsa, kwamitin da aka hada don bincike kan ayyukan sanatan ne ya yanke hukuncin dakatar da sanatan a matsayin matakin farko na ladabtarwa, rahoton Sahara Reporters.
Martanin zababben sanatan bayan sanar da korarsa
A lokacin da aka tuntube shi, David Jimbuta ya ce:
“Wadanda suka sanya hannu kan takardar korar mara tushe ba mambobin jam’iyyar bane. Don haka, ban damu ba."
Rahotanni a baya sun bayyana cewa, akwai kitimurmura a game da kujera da tikitin sanatan Taraba ta Kudu a APC tsakanin zababben sanatan da kuma Usman Danjuma Shiddi.
Jimkuta ya maka Shiddi a kotu game da sakamakon zaben fidda gwanin da aka yi, inda daga baya ya yi nasara.
An dakatar da Amos ne a daidai lokacin da ake ci gaba da shirin rantsar da zababbun ‘yan siyasan da suka yi nasara a zaben bana.
Ya zuwa yanzu, jam’iyyar APC ta bayyana dalilin dakatar da sanatan tare da bayyana yadda ya gaza kare kansa a gaban wani kwamiti.
BY ISYAKU.COM