An kayyade kudin aikin hajjin 2023 akan N2.8m ga kowane mahajjaci


Hukumar alhazai ta kasa NAHCON ta bayyana kudin aikin hajjin kowane maniyyaci na shekarar 2023 akan N2.89m.

 Shugaban Hukumar NAHCON, Zikrullah Hassan ne ya bayyana hakan a ranar Juma’a, inda ya danganta hauhawar farashin kayayyaki a Najeriya da Saudiyya. Daily trust ta rahoto.

 Hassan ya ce farashin ya kai nau’i 8, inda jihohin Borno da Yobe ke kan gaba yayin da Jihohin Legas da Ogun suka fi Naira miliyan 2.99.

 Daily trust ta ruwaito cewa karin kudin ya haura N300,000 idan aka kwatanta da wanda aka biya a aikin hajjin 2022.

 “Kudin aikin Hajji yana da nau’i 8 daban-daban, mahajjata daga Maiduguri da Yola, za su biya 2.89m sauran jihohin Arewa 2.919m. 

 Yankin kudancin kasar nan yana da farashi daban-daban guda shida, jihar Edo da sauran jihohin Kudu maso Kudu da Kudu maso Gabas za su biya N2.96m yayin da jihohin Ekiti da Ondo za su biya N2.88m, jihar Osun kuma za ta biya N2.99m.  

Cross River za ta biya N2.943m sai Legas, Ogun da Oyo su biya N2.99m,” inji shi.

 Ya bayyana rashin daidaiton farashin ne saboda jihohin arewacin kasar sun fi jihohin Kudu kusanci da Saudiyya sannan kuma matsugunin da kowace jiha ta samu shi ma ya nuna adadin kudin da za su biya.

 Ya ce kamfanonin jiragen da aka amince da jigilar maniyyata daga jihohi su ne;  Air Peace, Azman Air, Fly Nas, Aero Contractors da Max Air yayin da Arik Air da Value jet aka amince da su a matsayin hayar jirage masu zaman kansu.

 Ya kuma kara da cewa hukumar za ta rufe tashar ga wadanda suka zabi shirin ceto aikin hajji kafin ranar 21 ga watan Afrilu.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN